Gwamnan jihar Zamfara Muhammad Bello Matawalle, ya buƙaci a tsawaita wa’adin ritayar jami’an sojin Najeriya, da ‘yan sandan Najeriya da sauran hukumomin tsaro zuwa shekaru 70.

Gwamnan ya yi wannan jawabi ne a ranar Lahadin a garin Maradun lokacin da ya karbi bakuncin gamayyar kungiyoyin fararen hula da suka gudanar da wani gangamin lumana domin nuna goyon baya ga manufofin gwamnatinsa na tsaro na baya-bayan nan kan mazauna jihar rike makamai.

Ya ce idan har gwamnatin tarayya za ta iya tsawaita wa’adin ritayar likitoci da malaman jami’o’i da alkalai, yana da kyau a aiwatar makamancin hakan ga jami’an tsaro.

Matawalle ya koka kan yadda akasarin jami’an tsaro ke yin ritaya a wani mataki da ake bukatar ayyukansu.

Matawalle ya ce ya kamata Gwamnatin Tarayya ta duba shekarun ritayar Sojoji da ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro da nufin tsawaita wa’adin zuwa shekaru 70 kamar na bangaren shari’a da malaman jami’o’i da kuma fannin kiwon lafiya.

Gwamnan ya koka a kan yadda ya ke ɗaukar matakan da gwamnatinsa ta dauka na kawo karshen ‘yan fashi, lamarin ya ci tura.

Leave a Reply

%d bloggers like this: