Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi a Najeriya NDLEA ta tabatar da kama wani Sulaiman Idi da ake zargi ya tsere daga gidan yarin Kuje bayan mayakan ISWAP sun kai hari ranar Talatar makon da ya gabata.

Mai magana da yawun hukumar Femi Babafemi ne ya sanar da haka ya ce an kama Sulaiman a Maiduguri ta jihar Borno yayin da ya ke tare abin hawa.
Ya ce wanda ake zargin an sameshi da kayan maye kuma ya tabbatar musu da cewar ya tsere ne daga gidan yarin bayan an kai hari.

Haka kuma a Suleja yan sanda sun samu nasarar kama wani Kazeem Murtala da ake zargi ya gudu daga gidan yarin Kuje a Abuja

Mai magana da yawun yan sandan jihar DSP Wasiu Abiodun ya tabatar da kama mutumin mai shekaru 54 a ranar Asabar karshen makon da ya gabata.
Ya ara da cewar jami’ansu sun samu nasarar kama wanda ake zargin ne bayan da ya an kama wanda ake zargin ya tabbatar da cewar ya na daga cikin mutanen da su ka tsere daga gidan yarin Kuje.
Idan ba a manta ba rundunar yan sandan jihar Nassarawa ma ta tabatar da kama wani daga cikin mayakan Boko Haram da su ka tsere daa gidan yarin Kuje a makon da ya gabata.