Kamfanin rarraba hasken wutar Lankarki na Najeriya reshen KEDCO Jihar Kano ya bayyana cewa a yau Asabar za ai rashin wutar lankarki na tsawon awanni Takwas a Jihar.

Jami’in hulda da jama’a na Kamfanin Ibrahim Sani Shawai ya bayyana cewa za a fuskanci ƙarancin wutar lantarkin ne daga karfe 10 na safiya zuwa ƙarfe 6:30 na yammacin ranar sakamakon gyaran wutar lantarkin da za su yi a unguwar Kumbotso.
Shawai ya kara da cewa za su yi gyaran ne domin samar da wutar lantarkin yadda ya kamata ga abokan huldar kamfanin.

Kamfanin ya bayyana wa al’umma cewa da zarar sun gama gyaran wutar za su kunna wutar domin al’umma su ci gaba da amfana.
