Wasu mahara sun hallaka Hon Isyaku Bakano a gidan sa da ke karamara hukumar Song a Jihar Adamawa.

Lamarin ya faru ne a daren jiya Juma’a a lokacin da maharan su ka kutsa kai gidan nasa.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jihar Sulaiman Yahya Nguruje shine ya bayyana faruwar lamarin.

Kakakin ya bayyana cewa bayan da “yan bindigan su ka harbe kansilan an mikashi izuwa asibiti kuma a nan aka tabbatar da mutuwarsa.

Nguroje ya ce a lokacin da yan bindigan su ka shiga gidan kansilan sun harbi dan sa daya, inda ya ce shima an mikashi asibiti domin kula da lafiyar.
Hon Siyaku Bakano ya kasance kansila mai wakillar mazabar Gudu mboi a karamar hukumar Song ta Jihar Adamawa.