Gwamantin tarayya ta bayyana cewa ta na kokarin ta na kubutar da fasinjoji jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja da aka yi garkuwa da su a Maris.

Sabon ministan sufuri injiya Ma’azu Jaji Sambo shine ya bayyana haka a jiya bayan zanga_zangar da jama a su kayi a ofishin sa.
Sambo ya ce akwai abubuwan da gwamanti ba sai ta fada ba a bainar jama a, amma su na kokari ganin sauran mutane 43 da ke hannun yan bindiga sun kubuta.

Ministan ya ci gaba da cewa jama a su kwantar da hankalin su da zarar ya fara aiki zai ci gaba da binciken kamar yadda ake yi yanzu haka.

Minista Ma’azu Jaji Sambo ya samu sauyin mukami daga karamin ministan ayyuka zuwa ministan sufuri wanda ya samu rantsuwa a ranar 7 ga watan Yuli da muke ciki.
Sannan mutane sun isa ofishinsa a jiya Litinin dauke da kwallaye dauke da rubuta cewa gwamanti ta ceto yan uwansu daga daji.
A watan Maris din shekarar da muke ciki ne wasu da ake zargin yan bindiga ne suka tare jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja tare da yin yij garkuwa da mutane akalla 70 yayin da daga bisani su ka saki wasu daga ciki.