Gwamnatin tarayya ta ce za ta ɗauki matakin doka a kan gidan talabiji na BBC da Trust TV  bisa rahotannin da su ka yaɗa a kan ƴan bindiga.

Gidan talabijin  na Trust TV sun fara tattaunawa da fitaccen ɗan bindiga Bello Turji da wasu ƴan bindiga da kuma wasu mutane a kan halin da su ka shiga a sanadin hare-haren ƴan bindigan.

A kwanann nan gidan talabiji na BBC ya ɗakko wani bidgiyon ƴan bindigan a cikin daji har su ka tattauna da fitaccen ɗan bindigan da ke nema ruwa a jallo Ado Aleru.

Minstan yaɗa labarai da akl’adu a Najeriya Lai Mohammed ya tabbatar da cewar gwamnati ba za ta zuba idanu gidajen talabiji su ci gaba da tallata ayyukan ƴan bindiga ba.

Sannan wajibi ne su ɗauki mataki kamar yadda dokar hukumar kafafen watsa labarai ta samar  kuma su ka karyata.

A cewar ministan, yayin tattaunawa da manema labarai a yau Alhmis a Abua, ya ce gwamnatin Najeriya za ta ɗauki matakin da ya dace a dangane da gidajen talabijin guda biyu.

A cikin bidiyoyin da gidajen talabijin su ka nuna, sun bayyana yadda gwamnati ke baiwa ƴan bindiga kuɗin fansa musamman a jihar Zamfara, sai dai gwamnatin a baya ta musanta hakan.

Gidajen talabijin guda biyu sun nuna halin da mutane ke shiga a sanadin ayyukan ƴan bindiga, tare da ji daga yan bindigan a kan dalilin da ya sa su ke hakan da kuma abinda su ke buƙata domin ajiye makamansu yadda za a kawo ƙarshen ayyukan su baki ɗaya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: