Gwamna Jihar Borno, Babagana Zulum ya bayyana fargaba kan karancin kudi da talauci, idan ba a magance shi ba, na iya tilasta wasu mutanen da ke sansanin gudun hijira shiga ƙungiyar Boko Haram da ISWAP.

Gwamnan, wanda ya bayyana hakan a yayin rufe sansanin yan gudun hijira na Dalori-1, Dalori-2 Gubio da Muna a Maiduguri, ya ce gwamnati ba za ta iya cigaba da ajiye mutanenta a sansanin yan gudun hijirar ba.
Ya ce jihar, a karkashin jagorancinsa za ta yi duk mai yiwuwa domin ganin an mayar da mutane gidajensu cikin mutunci.

Zulum ya ce hanya guda da za a magance matsalar yan ta’adda shine gwamnati ta magance silar abin wanda ya hada da karuwar talauci, rashin ababen cigaba da matsalar dumamar yanayi.

Gwamnan ya ce za a rufe dukkan sansanin yan gudun hijira kafin wa’adin gwamnatinsa ya kare yana mai kira ga gwamnatin tarayya ta taimaka ta hanyar rage dogaro kan tallafin da ake bawa yan gudun hijirar na matsakaicin zango da dogon zango.