Shugaban Najeriya Muhamamdu Buhari yace a halin da ake ciki babu wata ƙasa guda ɗaya da bata fuskantar ƙalubale a ɓangaren tsaro.

Shugaban ya bayyana hakan ne yayin tarbar sabbin  jakadun ƙasashen Canada James Kingston Christoff da Mexico Juan Alfred Miranda  a Najeriya  yau a Abuja.

Shugaba Buhari ya jinjinawa jami’an staro a bias aikin dasu ke tuƙuru don tunkarar matsalar tsaro da ƙsar ke ciki.

Sannan ya ce gwamnatins ana aiki da sauran ƙasashen da ke maƙobtaka da juna kuma ana sa ran samun ɗumbin nasara mai away a nan gaba.

Ya ƙara d acewa ɓullar annobar Korona ta haifar da koma baya a sha’anin tattalin arziƙin ƙasashen duniya kuma ana ƙoƙarin ganin an farfaɗo da arziƙin ƙasa.

Ya ce a halin da ake ciki Najeriya na fuskantar matsalolin tsaro daga masu garkuwa da ƴan bindiga har ma da mayaƙan Boko Haram sai dais u na iya ƙoƙarinsu don ganin an shawo kan lamarin.

A nasa jawabin, babban kwamishinaa ƙasar Canada ya yabawa shugaban tare da tabbatar da cewar za su yi aiki kafaɗa da kafaɗa don ganin an samu nasara tare da bayar da dukkan gudunmawa a Najeriya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: