Wata babbar kotu a jihar Ekiti ta ta yankewa wasu ƴan fashi biyu hukuncin kisa ta hanyar rataya.

An samu yan fashin da aikata laifuka guda shida kowannensu.
Tun a ranar 6 Oktoban shekarar 2021 aka samu mutanen biyu da aikata fashi kuma su ka kwace wayoyin hannu da kuɗi naira 31,000.

Sannan a ranar sun yi garkuwa da wata Adejuwoj Daramola sannan su ka yi mata fyaɗe.

Sannan mutanen sun yi amfani da bindiga da adda yayin aikata ta’addancin.
Masu gabatar da ƙara sun gabatarwa da kotu shaidu wanda ta tabbatar da cewar mutanen sun aikata laifin.
Mai shari’a Justice Olalekan Olatawura ya gamsu da dukkanin hujjojin da aka gabatarwa da kotu tare da yankewa mutanen hukunci.
A cikin hukuncin kotun, ta tabbatar da cewar mutanen sun aikata fashi da makami kuma a sakamakon hakan aka yanke musu hukuncin kisa ta hanyar rataya.