Wasu da ake kyauta zaton yan bindiga ne suns ace wata mara lafiya daga gadon asibiti a Zariya ta jihar Kaduna.

Ƴan bindigan suns ace matar ne a wani asibiti da ke Anguwar Malamai da ke karamar hukumar Zariya.
Ƴan bindigan sun je asibitin ne da misalin karfe 12:00am na daren ranar Laraba wayewar yau Alhamis.

Ƴan bindigan sun yi niyyar saace wani Alhaji Shuaibu Dalhatu miji ga mara lafiyar, sai dai kasancewarsa a farke ba bacci yake ba ya sa ya gudu su kuwa su ka tafi da matarsa.

Wani mazaunin garin ya sake tabbatar da cewar ƴan bindigan sun yi ta harbe-harbe kafin ɗauke mara lafiyan.
Hukumomi a jihar Kaduna ba su ce komai a dangane da lamarin ba.
Jihar Kaduna na fama da rikicin ƴan bindiga da mayakan Boko Haram, ko a makon d amunke cikj sai da yan bindiga su ka kai wa tawagar mataimakin sufeton yan sanda hari tare da hallaka dogarinsa.
