Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta ce tsawaita aikin rajistar masu kada kuri’a zai kawo cikas ga shirye-shiryenta na zaben 2023.

Hakan ya fito ne a cewar kwamishinan zabe na jihar Akwa Ibom Mike Igini wanda ya yi magana yayin wata hira da gidan talabijin na Channels.
Ya ce Yanzu da suka dakatar da aikin rijistar a hukumance, dole ne su ƙarfafa tattara bayanai don ganin sun samarwa da yan kasa rijistar.

Sannan hukumar zabe za ta fara raba katin zabe na dindindin (PVCs) ga sabbin masu rajista.

Ya ce akwai sauran abubuwa da yawa da ya kamata a yi, sannan ya ce sashe na 17 na dokar zabe ne kawai ya umurci Hukumar ta dakatar da rajistar masu kada kuri’a kasa da kwanaki 90 kafin zaben.
Igini ya ce ya kamata ‘yan Najeriya su damu da fitowar masu kada kuri’a a zabe mai zuwa duk da kukan da aka yi na dakatar da rajistar.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta bayyana gamsuwarta da yadda ‘yan Najeriya ke sha’awar gudanar da zabe a baya-bayan nan, inda ta kwatanta hakan da abin da ya faru a kasar tun kafin zaben 1993.
An dakatar da rijistar zabe ga ƴan Najeriya a ƙarshen watan da ya gabata domin kammala aikin samar da katin zaɓe ga waɗanda su ka yi rijistar.
