Karamin Ministan gwado na Najeriya Festus Keyamo ya tabbatar da cewa gwamnatin tarayyar Najeriya ba ta da ikon ciyo bashi har naira Tiliyar 1.2 a duk shekarar domin ta biya wa malaman jami’a ta ƙasa ASUU bukatunsu.

Keyamo ya bayyana hakan ne a jiya juma’a a lokacin da ya amsa wasu tambayoyi a gidan Talabijin na Channels.
Ministan ya ce sakamakon buƙatun da kungiyar malaman Jami’a ta ASUU ke so abiya musu hakan ba zai sanya gwamnatin tarayya ta ciyo bashin har na naira Tiriliyan 1.2 domin ta biya musu buƙatunsu.

Keyamo ya kara da cewa a yanzu idan aka yi duba da kudin shiga da kasar ke samu bai wuce Naira Tiriliyan 6.1 a lokacin da ake da hanyoyin cibiyoyin kiwon lafiya wanda za a gina su da kuma sauran wasu bangarorin da ke da bukatar kulawa.

Karamin ministan ya ce ya kamata kungiyar ta ASUU ta koma su ci gaba da ayyukan su domin ba su kadai ne wadanda su ke karkashin gwamnati ba.
Kiyamo ya ce don haka kasar ba za ta tsaya ta daina gudanar da ayyukan ta ba a kan rashin ƙin bibiyawa ƙungiyar buƙatunsu.
Sananan Fetus Keyamo ya yi kira ga iyayen daliban da su ke a jami’a da su roki kungiyar ta ASUU ta taimaka ta janye daga yajin aikin da ta ke ciki a Najeriya.