Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya gargaɗi ƴan Najeriya a kan zaɓen shekarar 2023 mai gabatowa.

Obasanjo ya gargaɗi ƴan ƙasar da kada su yi kuskuren zaɓen tmun dare domin hakan na iya sanyawa ƙasar ta ruguje bayan zaɓe.
Tsohon shugaban ya bayyana haka ne a wani taro da aka gayyaceshi a jihar Legas.

Shugaban ya ce hanyar da za ta sanya ƙasar ta samu ci gaba shi ne zaɓen shugabanni na gari waɗanda su ka cancanta.

Obasanjo ya ce Najeriya ba ta ɗaukar matakan da su ka kamata wajen yaƙi da Talauci da matsalar tsaro wand ya ke ciwa ƙasar tuwo a ƙwarya.
Watanni ƙasa da takwas su ka rage don gudanar da babban zaɓe a Najeriya a mataki daban-daban kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.