Shugaban hukumar Haliru Nababa ne ya aza harsashin ginin gidaje guda 160 a mKuje da ke babban birnin tarayya Abuja.

Hakan na zuwa ne bayan da hukumar ta fara ɗaukar sabbin dabarun aiki bayan kai hari gidan yari na Kuje a Abuja.

Shugaban ya ƙaddamar da ginin ne a ranar Talata da nufin ƙarfafa tsaro tare da bai wa ma’aikatan gidaje a kusa domin walwalarsu.

Sabon tsarin gina gidajen ma’aikatan za a yi ne a dukanin jihohin Najeriya cikin gidajen gyaran hali domin tabbatar da tsaro tare da ƙarfafawa ma’aikatan gwiwa.

Idan ba a manta ba mayaƙan Boko Haram sun kai hari gidan yari na Kuje a Abuja tare da kuɓutar da masu laifi ciki har da waɗanda ake zargi da shiga ƙungiyar Boko Haram.

Leave a Reply

%d bloggers like this: