Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya nada sabon mai magana da yawun masarautar Kano.

An naɗa Abubakar Balarabe Ƙofar Naisa a matsayin mai magana da yawun masarautar Kano.

Sanarwar hakan na ƙunshe a wata takarda mai dauke da sa hannun sakataren gwamnatin Kano Alhaji Usman Alhaji.

Abubakar Balarabe Ƙofar Naisa shi ne babban mataimaki na musamman ga gwamnan Kano a kan kafafen yaɗa labarai.

Kuma zai ci gaba da riƙe matsayin guda biyu kamar yadda sanarwar ta tabbatar.

Kafin hakan, Abubakar Balarabe ya kasance wakilin gidan rediyo Kano a ofishin mataimakin gwamnatin jihar Kano daga bisani ya zamto wakilin gidan rediyon a ofishin gwamna.

Abubakar Balarabe ya kasance wanda ya taɓa gabatar da fitaccen shirin na na Tarkar Labarai a rediyo Kano.

Leave a Reply

%d bloggers like this: