Ministan ilimi a Najeriya Malam Adamu Adamu y ace rashin biyan malaman jami’a albashi ne ya sa su ka gaza cimma matsaya a zaman sulhun da aka yi.

Malam Adamu Adamu ya bayyana haka ne a yau Alhamis yayin zaman gabatar da bayanai da aka saba yi a fadar gwamnatin tarayya.
Ya ce malaman jami’a sun buƙaci a basu haƙƙoƙinsu ciki har da albashin da gwamnatin ta rike tsawon lokacin da su ke yajin aikin.

Ya ƙara da cewa tsarin ba aikai babu albashi yay i aiki a kan malaman jami’an sanadin rashin aikin da bas a zuwa wanda hakan ya sa aka gaza cimma matsaya a zaman sulhun.

Sai dai y ace akwai wasu buƙatun da tuni aka cimma matsaya a kansu.
Ya ce a na sa ran kashi huɗu bisa biyar na kungiyoyin manyan makarantu a Najeriya sun amince za su koma bakin aiki nan da mako guda.
Sannan ministan ya bukaci ɗaliban jami’an da su gurfanar da malaman jami’a a gaban kotu domin nema haƙƙi a kan lokacin da aka ɓata musu.
Ya ce zaman ɗaliban a gida fiye da watani shida na damun gwamnatin sai dai babu yadda za ta yi ne a kai.