Kungiyar Izalatul Bidi’a ta Najeriya ta bukaci gwamnatin tarayya da ta gaggauna gudanar da bincike kan kisan Malam Goni Aisami na Jihar Yobe tare da hukunta wadanda su ka aikata kisan.

Shugaban kungiyar Sheikh Abdullahi Bala Lau shi ne ya bayyana hakan a lokacin da ya ke zantawa da gidan jaridan BBC inda ya ce kisan Malamin da batagari su ka yi ta’addanci ne.

Bala Lau ya kara da cewa Al’umar musulmi su na neman a yi musu Adalci akan kisan.

Sheik Bala Lau ya ce daga lokacin da aka yi rashin wani babban malamin aka tabbatar an yi asara mai girma.

Bala Lau ya ce abin takaici ne hanyar da mutanen su ka bi wajen kisan malamin wanda dukkan wanda ya ji sai ya nuna bacin ransa.

Sheik Abdallah Bala Lau ya ce kungiyar su ta na mai kira ga gwamnati da ta jajirce wajen ganin ta dauki matakin hukunci akan wadanda su ka aikata kisan.

Ya ce ba za su yi shiru ba akan kisan tare da neman hakkin malamin har sai an zartar da hukunci tare da tabbatar da shi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: