Dan takarar shugaban kasa a Jam’iyyar NNPP Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya bayyana dalilin da ya sa bai samu halattar taron kungiyar Lauyoyi ta Kasa da aka gayyace shi ba.

Sanata Kwankwaso ya sanar da hakan ne ta cikin wata takarda da ya aikewa da kungiyar ta Lauyoyi NBA wanda mai magana da yawun sa Abdulmumin Jibril Kofa ya wallaf a shafinsa na Facebook.

Wasikar na dauke da ban hakuri ga kungiyar sakamakon wasu ayyuka da su ka hanashi zuwa.

Kwankwaso ya kara da cewa wakilin da zai turo domin ya wakikce shi Bishop Isaac ya tafi kasar waje ne hakan ya sanya bai turoshi gurin taron ba.

Rashin zuwan kwankwaso gurin ya haifar da kace-na -ce a shafukan sada zumunta.

Taron da kungiyar ta Lauyoyi ta gudanar shi ne babban taron ta na kasa wanda ta gudanar a garin Legas a ranar Litinin.

Kuma taron ya samu halattar masu ruwa da tsaki da manyan ‘yan siyasa har da yan takarar shugabanci a madafun iko dabqn-daban.

Leave a Reply

%d bloggers like this: