Shugaban kungiyar jami’o’i Najeriya ta kasa ASUU Farfesa Emmanuel Osodoke ya bayyana cewa wasu daga cikin jami’o’in a wasu Jihohin Najeriya na bogi ne.

Farfesa Emmanuel Osodoke ya bayyana hakan ne a lokacin da ake hira da shi a gidan Talabiji na Arise a ranar Alhamis.
Farfesa Osodoke ya ce dukkan wata jami’a da ba ta goyan kungiyar ASUU akan yajin aikin da ta ke yi ba mambar kungiyar ba ce.

Ya ce har yanzu jami’o’in da ke karkashin kungiyar ta ASUU su na ci gaba da gudanar da yajin aiki.

Tun bayan da Osodoke ya bayyana hakan ya haifar da cece-kuce a tsakanin mutane da kuma wasu jami’o’in jihohin Najeriya.
Wasu daga cikin jami’o’in da su ka koma bakin aiki sun nuna rashin jindadin su dangane da wannan kalamai na Osodoke tare da neman ya ba su hakuri.