Hukumar tsaro ta fararen hula a Najeriya NSCDC ta tabbatar da cewa jami’an hukumar sun kwace motoci 300 wadanda ake yin amfani da su a haramtattun matatun mai a fadin Najeriya.

Shugaban hukumar Ahmad Abubakar Audi shi ne ya bayyana hakan a yayin wani taro da su ka gudanar da kwamandojin hukumar.

Audi ya ce hukumar ta su ta samu nasarar lalata matatun mai guda 50 tare da kama mutane 200 wadanda su ke da hannu a cikin shekara guda.

Kwamandan ya kara da cewa sun yi hakan ne sakamakon yawaitar satar mai da ake yi

Hukumar tsaro ta fararen hula a Najeriya NSCDC ta tabbatar da cewa jami’an hukumar sun kwace motoci 300 wadanda ake yin amfani da su a haramtattun matatun mai a fadin Najeriya.

Shugaban hukumar Ahmad Abubakar Audi shi ne ya bayyana hakan a yayin wani taro da su ka gudanar da kwamandojin hukumar.

Audi ya ce hukumar ta su ta samu nasarar lalata matatun mai guda 50 tare da kama mutane 200 wadanda su ke da hannu a cikin shekara guda.

Kwamandan ya kara da cewa sun yi hakan ne sakamakon yawaitar satar mai da ake yi da kuma fasa bututu wanda hukumar ke korarin dakike faruwar hakan kuma hakan ya sanya ta shirya taron domin samo hanyoyin da za a magance faruwar hakan.

Taron ya gudana ne tare kwamandojin hukumar da kuma shugabannin sashen yaki da fasa bututun mai.

Sannan an tattauna kan yadda za a kawo karshen matsalar a fadin Najeriya.

Audi ya bayyana cewa ya zuwa yanzu hukumar ta fara yin binciken sirri akan rundunar ta mai yaki da satar mai da kuma fasa bututu a Najeriya.

kuma fasa bututu wanda hukumar ke korarin dakike faruwar hakan kuma hakan ya sanya ta shirya taron domin samo hanyoyin da za a magance faruwar hakan.

Taron ya gudana ne tare kwamandojin hukumar da kuma shugabannin sashen yaki da fasa bututun mai.

Sannan an tattauna kan yadda za a kawo karshen matsalar a fadin Najeriya.

Audi ya bayyana cewa ya zuwa yanzu hukumar ta fara yin binciken sirri akan rundunar ta mai yaki da satar mai da kuma fasa bututu a Najeriya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: