Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta bayyana cewa a yayin zaben shekarar 2023 mai zuwa za a nuna yadda zaben zai gudana domin tabbatar da gaskiya a cikinsa a lokacin da za a kirga kuri’a.

Hukumar ta bayyana cewa a yayin zaben za ta dinga dora yadda sakamakon zaben ya ke gudana daga kowacce runfar zabe ta kafar Internet na shafin hukumar ta zabe kamar yadda aka gudanar a zabukan jihohin Ekiti da Osun.

Shugaban hukumar zabe na kasa Farfesa Muhammad Yakub shine ya tabbatar da hakan a jiya juma’a a taron kaddamar da rahoton kungiyar fafutukar Yiaga Africa kan zaben gwamnonin jihohin Osun da Ekiti.

Shugaban wanda ya samu wakilcin Barister Festus Okoye, kuma rahoton ya nuna yadda sakamakon binciken da aka gudanar kan yadda zabukan su ka kasance.

Hukumar ta kuma bayyana wa ‘yan Najeriya cewa a lokacin zaben komai za a gudanar da shi ne a fili ba tare da wani boye-boye ba ta yadda kowa zai gamsu da abinda ya ke gudana.

Leave a Reply

%d bloggers like this: