Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gana da shugabannin ƙungiyar gwmnonin jam’iyyar APC yau a Abuja.

Shugaba Buhari ya yi ganawar sirri da shugabannin ƙungiyar gwamnonin ne ba tare da ƴan jarida ba.

Bayan ganawar da shugabannin su ka yi da shugaba Buhari wasu daga cikin sun ziyarci ofishin mataimakin shugaban ƙasa Farfesa Yemi Osinbajo.

Sai dai gwamnonin sun ƙi bayyanawa ƴan jarida abin da su ka tattauna da shugaba Buhari da mataimakinsa.

A na zargin gwamnonin sun gana da shugaban ne domin gabatar da tsare-tsaren da su ke yi don tunkarar zaɓen shekarar 2023.

Daga cikin gwamnonin da su ke halarta akwai shugaban  ƙungiyar gwamnonin APC Atiku Bagudu da gwamnan jihar Legas sai gwamnnan jihar Ekiti.

Sauran su ne gwamnan jihar Neja mataimakin  gwamnan jihar Ebonyi gwamnan jihar Ogun gwamnan jihar Jigawa gwamnan jihar Gombe da gwamnan jihar Nassarawa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: