Gwamnatin jihar Borno ta ƙaddamar da tsarin mayar da yaran da su ka tagayyara a sanadin rikicin Boko Haram zuwa makarantu.

Gwamnan jihar Babagana Umara Zulum ne ya ƙaddamar da tsarin a garin Monguno tare da ganawa da waɗanda rikicin ya shafa.

Bayan ƙaddamar da tsarin, an yi wa yara dubu bakwai rijista domin mayar da su makarantun firamare da sakandire a jihar.

Gwamna Zulum ya ce wannan matakin da aka fara kashi na farko ne daga cikin tsarin da za a ci gaba da yi domin mayar da yara marayu makarantu, waɗanda su ka rasa iyayensu a sanadin rikicin Boko Haram.

Rikicin mayaƙan Boko Haram ya yi silar jefa yara aƙalla sama da 200,000 maraici wanda kuma har yanzu aka gaza shawo kan lamarin.

Gwamnatin ta ce za ta gina sabbin makarantu domin mayar da marayun tare da basu tallafi a ɓangaren karatun domin ƙafafa musu gwiwa.

Rikcin Boko Haram ya fi ƙamari a jihar Borno wanda aka rasa rayuwan mutane da dama tare da lalata wurare daban-daban a jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: