Shugaban kasar Najeriya Muhammad Buhari ya bayyana wa gwamnonin jam’iyyar APC cewa ba zai sanya baki a zaben shekarar 2023 mai zuwa.

Mai magana da yawun shugaban Femi Adesina shi ne ya bayyana hakan bayan kammala tattaunawar da shugaban yayi da gwamnonin a fadarsa da ke Abuja a jiya Talata a wata ziyara da su ka kai masa.
Adesina ya ce shugaban ya bayyana wa gwamnonin cewa rashin sanya baki a zaben ya na nuna tsarin siyasa.

Shugaban ya ce hakan zai tabbatar da adalci da gaskiya da nutsuwa ga masu yin zabe kuma jam’iyyar ta mutun ta masu yin zabe.

Shugaba Buhari ya bayyana cewa kamar zaben da aka gudanar na gwamnonin Jihar Osun da Ekiti da kuma Anambra bai sanya baki a cikin sa ba.
Shugaban ya ce ya na girmama ‘yan Najeriya sannan kuma za a basu damar zabar wanda ransu ya ke so a babban zaɓen shejarar 2023 mai gabatowa.