Gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta sanya hannu a kan wata yarjejeniya domin bunƙasa bangaren lafiya a jihar.

Gwamnatin Kano ta sanya hannu a yarjejeniyar tsakaninta da ƙungiyoyin Ɗangote, Bill Melinda Gates Foudantion, da ƙungiyar da asusun tallafawa kananan yara na majalisar dinkin duniya wato UNICEF.

Yarjejeniyar da aka ƙulla a dakin taro na Africa Hose da ke fadar gwamnatin Kano, ya samu halartar shugaban hukumar lafiya matakin farko na ƙasa, da wakilai a hukumar lafiya ta duniya wato WHO.

A wata sanarwa da babban sakataren yaɗa labaran gwamnan Kano Malam Abba Anwar ya sanya hannu ranar Laraba, sanarwar ta ce ƙungiyoyin sun yaba ga yadda gwamnatin Kano ke tafiyar da al’amuran bangaren lafiya wanda hakan ya sa gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya zamto gwarzo a ɓangaren yaƙi da cutar Korona, lambar yabon da aka bai wa gwamnan kwanaki kadan da su ka gabata a babban birnin tarayya Abuja.

Yarjejeniyar ta ƙunshi ci gaba da ayyukan bayar da riga-kafin cutuka da kuma kara bunƙasa bangaren lafiya domin kula da jama’a.

A jawabin gwamnan Kano, ya sha alwashin ci gaba da karfafawa ɓangaren lafiya matakin farko da mataki na biyu domin ganin yadda ake samun nasara a karkashin jagorancinsa.

Sannan gwamnatin za ta tabbatar da cika alkawuran da aka kulla a yarjejeniyar tsakaninta da ƙungiyoyin.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: