Jami’ar IBBU da ke Jihar Neja ta bai wa Malaman jami’ar Umarnin komawa bakin aiki a ranar biyar ga watan Satumba mai kamawa.

Mataimaki a bangaren yada Labarai na makarantar Alhaji Baba Akote ne ya fitar da sanarwar hakan.
Sanarwar ta umarci malaman da su koma bakin aiki tare da yin fatali da yajin aikin da kungiyar ASUU ke yi.

Hukumar ta ce bayan komawar za a fara karatun zango na biyu na shekarar 2021 zuwa 2022.

Sanarwar ta kuma bai wa daliban makarantar da su koma makaranta domin ci gaba da daukar darasi wanda aka koma domin su.
Jami’ar Ibrahim Badamasi Babangida IBBU ta ce sun dauki matakin hakan ne a lokacin zaman da majalisar Amintattu na jami’ar ta yi zama na 55 a ranar Talata.
Shugaban Kungiyar ASUU reshen IBBU Dakta Kudu Dangana yayi martanin cewa yajin aikin da su ke yi yananan kamar yadda aka sani kuma ba za su koma bakin aiki ba.
Shugaban ya kara da cewa bayan sanar da komawa bakin aiki da jami’ar ta yi umarni su ka mikawa jami’ar wasikar tsawaita yajin aikin da su ke ciki na sai babatagani.
Dakta Kudu ya ce yayi mamakin yadda jami’ar ta fitar da sanarwar cewa za ta koma bakin aiki a ranar biyar ga wata mai kamawa.
Shugaban ya kuma shaidawa daliban jami’ar cewa dukkan wanda ya koma makaranta to tabbas zai yi asarar kudinsa ne da lokacin sa sannan kuma idan yaje makarantar ba zai samu kowa a cikin jami’ar ba.