Gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta kafa wani kwamiti wanda zai bibiyi dalilin rushewar wani gini mai hawa uku da ya ruhe a jihar.

Gwamnatin ta ƙaddamar da kwamitin ƙarƙashin jagorancin Rabi’u Sulaiman Bichi a dangane da benen da ya rushe a kasuwar waya ta Beirut ranar Talata.

Kwamitin da aka kafa yayin zaman majalisar zartarwa ta jihar.

Wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai na jihar Malam Muhammad Garba ya sanyawa hannu, ya ce kwamitin zai duba ko ginin ya cika ƙaidar da aka yi shi.

Ginin ya rushe a kasuwar siyar da wayar hannu ta Beirut ranar Talata tare da shafar mutane takwas.

Shugaban kasuwar Alhaji Ibrahim Rabi’u Tahir ya shaidawa Matashiya TV cewar ginin ba a kammalashi ba.

Yayin da mu ka tuntuɓi mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta ƙasa reshen jihar Kano Saminu Yusif, ya ce mutane takwas lamarin ya shafa kuma sun cetosu a raye ba tare da samun rahoton mutuwa ba.

A halin da ake cikin sun miƙa waɗanda abin ya shafa zuwa asibiti domin kula da lafiyarsu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: