Wasu ƴan bindiga sun yi garkuwa da Muhammad Ibrahim Tanko tsohon kansilan Gurdi da ke yankin Abaji a birnin tarayya Abuja da wasu daga cikin iyalansa su shida.

A yayin garkuwa da tsohon Kansilan ‘yan bindigan sun yi garkuwa da wasu mutane 11 a lokacin da su ka kai hari kauyen Tekpeshe a safiyar jiya Lahadi.
Wani mazaunin yankin mai suna Danlami Yakubu ya bayyana cewa ‘yan bindigan sun yi garkuwa da tsohon Kansilan ne a lokacin da ya je gurin wata ta’aziyya inda lamarin ya rutsa da shi.

A yayin harin ‘yan bindigan sun hallaka mutum daya.

Basaraken yankin Abaja Alhaji Abdullahi Adamu ya tabbatar da faruwar lamarin.
Inda ya ce Baturen yan sandan yankin ne ya shaida masa harin na ‘yan bidigan tare da sace Kansilan.
Kakakin rundunar ‘yan sandan birnin na Abuja DSP Adeh Josephine ba ta ce komai ba akan faruwar lamarin.
