Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta bayyana cewa fiye da mutane 700,00 ne su ke hallaka kawunan su a duk shekara a fadin Najeriya.

Wakilin hukumar a Najeriya Walter Kazadi Mulombo ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi ta cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar zagayowar tunawa da matakan kariya daga afkawa hadarin kashe kai ta duniya wanda ake gudanarwa a ranar goma ga watan Satumba kowacce shekara.

Walter ya ce kaso 77 cikin 100 na wadanda su ke kashe kawunan nasu su na yin hakan ne sakamakon matsalar karancin tattalin arziki.

Wakilin hukumar ya kara da cewa daga lokacin da wani ya kashe kansa akwai makamantan sa 20 da su ma su ke aikata hakan a daidai lokacin a wasu yankunan.

Walter ya ce hallaka kai ne na hudu a duniya wanda aka fi mutuwa ta hanyar sa musamman a tsakanin matasa ‘yan shekaru 15 zuwa 29.

Kazadi ya bayyana cewa hakan na haifar da damuwa ga ‘yan uwan wanda ya hallaka kan nasa da gwamnati harma da kasa baki daya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: