Wasu ‘yan bindiga sun hallaka mutane da dama tare da korar al’umma daga muhallansu a kauyuka sama da 21 da ke karamar hukumar Kebbe da ke Jihar Sokoto.

Shugaban karamar hukumar Hon Lawal Marafa Fakku ne ya tabbatar da hakan.

Lawal ya ce ‘yan bindigan sun kai harin ne a jiya Talata daga bisani kuma su ka kori mutane daga muhallansu a kauyuka fiye 21 da kuma mazabu uku cikin goma da ke yankin.

Fakku ya kara da cewa ‘yan bindigan sun shiga yankunan ne sakamakon yawaita kai hare-haren da jami’an tsaro su ke yi musu ne a Jihohin Zamfara Kebbi da kuma Neja domin samun gurin fakewa.

Kazaliza shugaban ya ce ya zuwa yanzu mutanen kauyukan na ci gaba da gudanar da bincike akan gano gawarwakin wadanda aka hallaka don sanin ‘yan uwansu.

Lawal Fakku ya ce ‘yan bindigan sun fara kai hare-haren yankunan ne a ranar Alhamis din da ta gabata.

Shugaban ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta taimaka ta kai musu jami’an tsaron soji domin korar ƴan bindigan daga yankunan.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Jihar Sunusi Abubakar ya tabbatar da cewa sun aike da jami’ansu yankunan domin fatattakar ‘yan bindigan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: