Hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya INEC ta yi gargaɗi ga ƴan siyasa da su guji yaƙin neman zaɓe a masallatai da coci-coci.

Hakan na daga cikin sabuwar dokar hukumar zaɓe da aka yi wa gyara a bana.
Babban lauyan hukumar Kayode Ajulo ne ya sanar da hakan yayin ganawa da kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN a Abuja.

Sannan ya buƙaci ƴan siyasa da su kiyaye karya doka musamman lokacin yaƙin neman zaben shekarar 2023 wanda aka fara a yau Laraba.

Ya ce sashe na 92 na dokar hukumar zaɓe ya haramta gudanar da yaƙin neman zaɓe a wasu wurare kamar masallatai da coci-coci.
Sannan an faɗaɗa hanyoyin yaƙin neman zaɓe wanɗanda babu su a baya.
Ya ƙara da cewa zagi ko kalaman ɓatanci ko waɗanda za su tayar da fitina ba sa daga cikin abin da hukumar ta lamunta kuma ta sake gargaɗin ƴan siyasa a dangane da hakan.
A watan Fabrairun shekarar da mu ke ciki ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sanya hannu a sabuwar dokar hukumar zaɓe wadda aka yi wa kwaskwarima.