Ƴan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyu daban-daban sun sanya hannu a kan tabbatar da zaman lafiya a Najeriya.

Masu neman ɗarewa a kujerar shugana ƙasa na jam’iyyar PDP, APC, LP, NNPP da sauran jam’iyyu sun halarci ɗakin taro na International Conference Center da ke Abuja tare da sanya hannu a kan goyon bayan zaman lafiya a zaɓen shekarar 2023.

Hakan na daga cikin tsarin da aka tanada domin tunkarar zaɓen shekarar 2023.

Ƴan takarar sun saka hannu da amincewar kaucewa duk wata hanya da ka iya kawo barazana ga zaman lafiya a Najeriya.

Tuni hukumar zaɓen mai zaman kanta a Najeriya INEC ta ɗage takunkumin tallan ƴan takara da yaƙin neman zaɓe a jiya Laraba.

A na sa ran za a gudanar da babban zaɓen ahekarar 2023 a ƙarshen watan Fabrairu da farkon watan Maris ɗin shejarar da mu ke ciki

Leave a Reply

%d bloggers like this: