Wata babbar kotu da ke zamanta a Jihar Legas ta yankewa wani basarake mai suna Michael Mitiu Yusuf da ke karamar hukumar Alimosho hukuncin zaman gidan gyaran hali na tsawon shekaru 15 sakamakon yin garkuwa da kansa da yayi a Jihar.
Alkalin kotun Hakeem Oshodo ya ce kotun ta yankewa basaraken hukuncin ne shi da wani mai suna Adams Opeyemi wanda ake zargin ya sa da taimaka wajen yiin garkuwa da kannasa.
Alkalin ya ce bayan yankewa basaraken hukncin da aka yi aka sallami matar sa.
Alkali Hakeem ya kara da cewa sun yanke masa hukuncin ne domin ya zama izinin ga masu shirin aikata hakan.
An kama basaraken ne tun a ranar 15 ga watan Yulin shekarar 2017 a lokacin da ya yi garkuwa da kansa domin ya haifar da rashin zaman lafiya a JIHAR.
Alkalin ya kara da cewa laifin da basaraken ya aikata ya saba da sashi na biyar wanda ya haramta yin garkuwa da mutane na Jihar shekarar 2017.
Tun bayan da aka kama basaraken da laifin yin garkuwa da kannasa gwamnaan wancan lokacin ya sauke shi daga kan mukaminsa kamar yadda sashi na 38 [1] na dokar da masarautun Jihar da ta tanadar.


