Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sake tabbatar da cewar gwamnatinsa ta yi duk abinda ya dace wajen ciyar da Najeriya gaba.

Muhammadu Buhari ya bayyana haka a cikin jawabinsa na zagayowar ranar samun ƴancin kai a Najeriya.
Shugaban ya ce gwamnatinsa ta yi ƙoƙari matuƙa wajen bunƙasa tattalin arziƙi da kuma tantance bayanai a kan asusun ajiyar banki ta ƴan ƙasar.

Haka kuma ya ce gwamnatinsa ta mayar da hankalin wajen bunƙasa aikin gona wanda hakan ya zamtowar ƙasar hanyar nasara duka a ƙarƙashin mulkinsa.

Shugaba Buhari ya ce ya na jin matuƙar ciwo a bisa yajin aikin da ƙungiyar Malamn jami’a su ka shafe fiye da watanni bakwai su na yi.
A ɓangaren yajin aikin, ya ce gwamnatinsa ta yi tsare-tsare da aka shafe fiye da shekaru 11 ba a yi su a a gwamnatocin baya.
Shugaban ya sake tabbatar da aniyarsa na ganin an gudanar da sahihin zaɓe a shekarar 2023.
Wannan ne karo na ƙarshe da shugaban ya yi jawabin tunawa da zagayowar ranar samun ƴancin kai a matsayinsa na shugaban ƙasa.