Rundunar ƴan sanda a jihar Jigawa sun tabbatar da cewar mutane 108 ne su ka mutu a sanadin ambaliyar ruwan sama a bana.

Lawal shiisu Adam mai magana da yawun ƴan sandan jihar ne ya bayyana hakan yau Asabar.

Jihar Jigawa na daga cikin jihohin da su ka fuskanci ambaliyar ruwan sama a bana wamda hakan ya yi sanadin lalacewar kuhalli da kuma rasa rayuka da dama.

Rahotanni sun ce ambaliyar ruwan sama ta fi tsanani daga watan Agusta zuwa yanzu.

Wasu ƙanan hukumomin da ambaliyar ta shafa akwai Kafin Hausa, Ringim, Birniwa, da ƙaramar hukumar Gumel.

Ambaliyar ruwan ta shafi gonaki da dama wanda hakan ya yi sanadin lalacewar amfanin gona da yawa daga ciki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: