Aƙalla mutane bakwai ne su ka mutu a sakamakon cin abinci mai guba a jihar Kogi.

Mai magana da yawun ƴan sandan jihar Williams Aya ne ya tabbatar da hakan ya ce mutane niyar daga ciki sun mutu nan take yayin da biyu su ka mutu daga bisani.
Al’amarin ya faru a ranar Litinin kuma an yi gaggawar kai wasu zuwa asibiti sai dai biyu sun mutu daga bisani.

Ko a ranar Lahadi sai da aka samu rahoton mutuwar mutane huɗu ƴan gida ɗaya bayan sun ci abinci da ake zargi mai guba ne.

Hukumar ƴan sanda a jihar ta ce ta samu labarin mutuwar mutanen waɗanda ake zargi sun ci abinci mai ɗauke da guba.
Sai dai wani rahoto ya nuna cewar an sake samun mutuwr mutane biyu da su ka ci abincin bayan an kai su asibiti wanda adadin waɗanda su ka mutu rnar Litinin su ka kai su tara.
