Kotun daukaka kara mai zamanta a Abuja, ta sanya yau Juma’a don yanke hukuncin game da ƙarar da ASUU ta shigar na ƙin amincewa da hukuncin da kotun masana’antu ta yanke.

A ranar 21 ga watan Satumba ne babbar kotun masana’antu ta ba da umarni ga Ƙungiyar da su koma bakin aiki kafin warware takaddamar da ke tsakaninsu da gwamnatin tarayya.

Lauyan kungiyar yace ba su gamsu da hukuncin da karamar kotu ta bayar ba, shine suka shigar da ƙara don ƙalubalantar gwamnati da nuna rashin dacewar kotun ƙasa wajen saurarar karar.

Ya ce yana daga cikin haƙƙin wanda ake ƙara, shigarwa ko ɗaukaka ƙara muddi hukuncin da akai masa bai masa ba.

Babban Lauyan wanda ya shaidawa Mai shari’a Hamma Barka wanda ke cikin mutum Ukun da ke sauraron ƙara, kan suyi watsi da ƙarar ko tuhumar da gwamnatin ke yiwa ASUU, sannan kuma a tabbatarwa da ƙungiyar damarta na daukaka ƙara.

Lauyan yana mai ƙara nusantar da Mashar’anta kan irin tanadin dokoki da tsarin shari’a da ASUU ke da shi kan gwamnatin tarayya.

Yayin da Lauyan gwamnati ke yi wa kotu bayani, Igwe ya bayyyanawa kotu rashin dacewar saurarar karar Ƙungiyar tare da tabbatar da cewa kungiyar bama ta bi ƙa’idoji ba wajen ɗaukaka kara.

Daga Ƙarshe dai alkalin kotun ya sanar da Yau, 7 ga watan Oktoban wannan shekarar a matsayin ranar yanke hukunci.

A zaman na yau alƙalin ya sake umartar ƙumgiyar malaman jami’a da su koma bakin aiki tare da dakatar da yajin aikin da su ke yi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: