Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ware naira biliyan 3.34 a matsayin kudaden da shugaba Buhari da mataimakinsa za su kashe wajen tafiye-tafiyen a Najeriya da kasashe ketare.

Hakan na ƙunshe cikin daftarin kasafin kudin shekarar 2023 mai zuwa wanda shugaban ya gabatar a gaban zauren majalisar Dattawan kasar a ranar Juma’a.
Shugaban da mataimakin za su kashe naira biliyan 2.49 domin yin tafiye-tafiye.

A yayin tafiye-tafiyen shugaban iya cikin gida Najeriya zai kashe Naira miliyan 862,076,448 yayin da tafiye-tafiyen kasashen ketare za su lamushe N1,633,464,208.

A bangaren mataimakin Shugaban Farfesa Yemi Osinbajo tafiye-tafiyensa zai kashe jumullar kuɗi N846,607,097.
A yayin tafiye-tafiyen cikin gida da Osinbajon zai yi za su kashe naira Miliyan 330,320,396 yayin da tafiye-tafiyen kasashen ketare kuma zai kashe naira 516,286,701.