Tsohon shugaban jam’iyyar hamayya ta PDP na kasa Vincent Ogblafor ya rigamu gidan gaskiya a kasar Canada.

Jaridar Vangaud ta rawaito Vincent ya mutu ne a ranar Alhamis yana da shekara 73.
Tsohon shugaban wanda ya kasance dan asalin garin Olokoro cikin karamar hukumar Umuahia ta Jihar Abia shine Sakataren jam’iyyar PDP na farko.

Kafin mutuwar tsohon shugaban an tilasta masa yin ritaya daga mukaminsa sakamakon rashin jituwa da ya shiga tsakanin sa da wasu jiga-jigan jam’iyyar.

Daga bisani kuma aka zargi Cif Ogbulafor ya yi almubazzaranci da kudade a lokacin da ya ke riƙe da mukamin minista.