Aƙalla mutane biyu ne su ka mutu yayin wani hari da ƴan bindiga su ka kai wani asibiti a jihar Neja.

Al’amarin ya faru a ranar Litinin da daddare a ƙaramar hukumar Lapai ta jihar.
Maharan sun kutsa ka cikin asibitin Abdussalam Abubakar da ke garin Gulu a jihar Neja.

A lokacin da su ka kai harin sun tafi da marsa lafiya da masu aikin jinya da kuma baban likitan asibitin.

Jaridar Daily Trust ta gana da wani ma’aikacin asibitin wanda yatabbatar da faruwar lamarin tare da tabbatar da sace marasa lafiyan.
Da aka tuntuɓi ƴan sanda a jihar ba su ce komai a dangane da harin ba.
Gwamnatin tarayya dai ta sha alwashin kawo ƙarshen matsalar tsaro a ƙasar zuwa watan Disamban shekarar da mu ke ciki.
