Hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya INEC ta gayyaci jagororin ƴan siyasa dangane da riki a lokacin yaƙin neman zaɓe.

Ana zargin wasu ƴan siyasa na far wa wasu a lokacin yaƙin neman zaɓe a wasu jihohin Najeriya.
Shugaban hukumar Farfesa Mahmood Yakubu neya gayyaci shugabannin jam’iyyu domin sanya hannu a kan yarjejeniyar zaman lafiya.

A yayin wani shirin horas da jami’an zaɓe na wucin gadi ta shirya dangane da zaɓen shekarr 2023 domin nuna musu haanyar amfani da sabbin na’urorin da hukumar ta tanada, shugaban hukumar Farfesa Mahmud Yakubu yace ƴan sanda za su kashe naira biliya 13 domin siyan makamai gabanin zaɓen.

Tun a baya hukumar zaɓe ke gargaɗin ƴan siyasa dangane da farwa junansu da kalaman tunzuri.
A ranar 28 ga watan Satumba aka ɗagee takunkumi ga ƴan siyasa a dangane da yaƙin neman zaɓe a faɗin Najeriya.