Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa a Najeriya NCDC ta ce zazzaɓin Lassa na ci gaba da bazuwa a sassan Najeriya.

A wani rahoto da hukumar ta fitar, ta ce a yanzu cutar ta tsallaka zuwa ƙananan hukumomi 104 na wasu jihohin Najeriya.
A shekarar 2022 zazzaɓin Lassa ya hallaka mutane 173 yayin da mutane 937 su ka kamu da cutar.

Hukumar ta ce kashi 71 na mutanen da su ka kamu da cutar sun fito ne daga jihar Ondo yayin da sauran jihohin Edo, da Bauchi ke bi musu baya.

Binciken hukumar da rahoton da ta fitar ya nuna cewa, cutar ta bazu zuwa jihohi 26 kuma ta harbi mutane a ƙanann hukumomi 105 na Najeriya.
Haka kuma mutanen da su ke tsaknain shekara 21 zuwa 30 cutar ta fi kamawa.
Sai dai a rahoton da ta fitar, ta ce babu wani ma’aikacin lafiya da ya kamu da cutar.
Hukumar ta ce ta na aiki da masu ruwa da tsaki don ganin an daƙile yaɗuwarta a dukkan mataki.