Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da auna kwazon ma’aikatun gwamnatinsa na kasa, inda ya bayyana cewa sun kaddamar da manyan ayyuka a sassa daban-daban na kasar nan domin cika wa ‘yan Najeriya alkawarin da suka yi musu.

Da yake magana kan sake shirya kwatanta kwazon da gwamnatinsa ta samu, shugaban kasa ya lissafo wasu daga cikin nasarorin da ya samu a bangaren gona da tattalin arziki da lafiya da yakar cin hanci da rashawa da dai sauransu.
Shugaban kasa ya shaida wa mahalarta taron ciki har da tsohon shugaban kasar Kenya, Uhuru Kenyatta cewa sama da hanyoyi da suka kai kimanin kilomita 3,800 ya gina a fadin kasar nan, yayin da aka saya wa rundunar sojojin saman Najeriya jiragen yaki har guda 38 domin fatattakar ‘yan ta’adda.

Ya kara da cewa ‘yan Najeriya miliyan 38.7 sun samu nasarar yin allurar riga-kafin Korona, wanda ya sa aka samu kashi 35 na yawan ‘yan Najeriya da suka yi riga-kafin cutar.

A bangren kayayyakin more rayuwa kuwa, shugaban kasar ya ce gwamnatinsa ta samar da muhimman ayyukan ci gaban kasa da farfado da tattalin arziki wanda ta bar kyakkyawar tarihi.
Ya ce, wasu daga cikin nasarorin da suka samu sun hada da kammala hanyar Itakpe zuwa Ajaokuta ta nufi Warri mai nisan kimomita 326 da titin dogo da ke tsakanin Lagas zuwa Ibadan mai nisan sama da kimomita 156.5 da kuma kammala babban aikin tashar jirgin ruwa da ke Apapa a Jihar Legas.
A bangren ayyukan hanya kuwa, wannan gwamnatin ta shiffida hanyoyi da suka kai kimomita 408 da gyara hanyoyin da suka kai kilomita 15,961 a dukkan sassa daban-daban da ke kasar nan.
A cewasa, gwamnatin tarayya a karkashinsa ta yi namijin kokari wajen samar da ayyukan ci gaban kasa a shekarun bakwan da ta shafe a kan karagar mulki. Buhari ya ce gwamnatin tarayya ta gina hanyoyin tarayya har guda 21 wanda suka kasance jimillar nisansu ya kai kilomita 1,804.6.
Shugaban kasar ya tabbatar da cewa gwamnatinsa ta yi kokari wajen bunkasa harkokin sufuri a filayen jiragen saman da ke fadin Najeriya.
Ya kara da cewa gwamnatinsa ta farfado da tattalin arziki wanda a baya ya samu koma-baya a wata ukun shekarar 2020.