Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya gabatar da kudirin kasafin kudin shekarar 2023 na Naira Tiriliyan 1.693 ga Majalisar dokokin jihar.

Daga cikin abubuwan da ake son kashewa a shekarar 2023, Naira tiriliyan 1.343 za ta samu ne daga kudaden shiga da ake samu daga cikin gida da na tarayya, yayin da za a samu gibin kudi na Naira biliyan 350 daga rancen waje da na cikin gida, da kuma lamuni da ake hasashen za su kasance cikin ma’auni na dorewar kasafin kudi na jihar.
A cewar gwamnatin jihar za ta ware jimillar Naira biliyan 67.4, wanda ke wakiltar kashi 3.98 na kasafin kudin shekarar 2023, domin cimma shirin gwamnati na samar da gidaje da samar da ababen more rayuwa a tsakanin al’umma.

Gwamnan ya ce jihar za ta ci gaba da zuba jarin da ya dace da kuma samar da ababen more rayuwa don ci gaba da bunkasar tattalin arzikinta fiye da shekara mai zuwa.

Babban abubuwan da gwamnatin jihar ke zata samu a 2023 sune kiwon lafiya da muhalli, ilimi, da tattalin arziki.
Sanwo-Olu ya bayar da shawarar ware Naira biliyan 153.5 ga ilimi a shekara mai zuwa, wanda ke wakiltar kashi 9.07 na jimillar kiyasin kasafin kudi, domin a dunkule nasarorin da aka samu a shekarun baya a fannin.
Ya ce jarin da aka zuba a baya a fannin ilimi ya yi nasara, wanda hakan ya sa aka samu gagarumat nasarar da aka samu na kashi 82 cikin 100 a jarrabawar kammala sakandare ta yammacin Afirka ta 2022.
Gwamnan ya ware naira biliyan 339 (kashi 20.06) domin samar da ababen more rayuwa a sassa daban-daban a shekara mai zuwa, yayin da ya ware jimillar Naira biliyan 191, wanda ke wakiltar kashi 11.29 bisa 100 na kiwon lafiya da muhalli.