Hukumar tsaron farin kaya ta DSS, da hukumar leken asirin Najeriya NIA, yan sanda da sauran jami’an tsaro sun kai harin kwantan bauna kauyukan Abuja tsre da kama wasu da ake zargi.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa jami’an tsaron sun garkame kwamandojin ISWAP biyar da mayaka 30 a unguwanni kamar Mararaba dake makwabtaka da kwaryar birnin tarayya Abuja.

Rahoton ya kara da cewa waɗanda aka kama suna tsare yanzu a ofishin hukumar DSS.

Bayanai sun nuna cewa hukumomin tsaron sun kwana biyu suna bibiyar yan ta’addan gabanin gargadin da Amurka da Birtaniya sukayi ranar Lahadi na cewa yan kasarsu suyi hattara.

Wata majiyar tsaro da tayi karin haske kan lamarin tace yan ta’addan na shirin kai munanan hare-hare Abuja kafin a kamasu.

Majiyar ta ce wadanda aka kama sun bada bayanai masu amfani wadanda suka taimaka wajen damke wasu mambobin ISWAP dake basaja da aikin ga ruwa, masu gadi, kanikanci, da sauran su.

Wani babban jami’in tsaro da aka sakaye sunansa ya bayyana cewa, ana gudanar da binciken kwa-kwaf domin kassara yan ta’addan ISWAP dake Abuja.

An damke kwamandojinsu da yawa da yaransu kuma suna taimaka musu wajen bincike.

Yayinda aka tuntubi Kakakin hukumar DSS, Peter Afunanya, ya bayyana cewa bai samu labarin haka ba har yanzu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: