Kotun daukaka kara dake zamanta a Abuja ta soke hukuncin da mai shari’a Iyang Ekwo na babbar kotu ya yanke a ranar 8 ga watan Maris na korar gwamna David Umahi da mataimakinsa.

An yi ƙarar gwamnan da mataimakinsa ne a kotu tun bayan da suka bayyana sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC.

A hukuncinta na yau Juma’a 28 ga watan Oktoba, kotun daukaka karar ta ce, babu inda kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanadi hukunci ga duk gwamna ko mataimakin da ya sauya sheka.

A hukuncin, mai shari’a Haruna Tsanami ya bayyana cewa, dama daya da ‘yan jam’iyyar da suka fusata suke da ita itace duba yiwuwar tsige gwamnan kamar yadda yazo a kundin tsarin mulkin kasa.

Hukuncin na kotun daukaka na Abuja dai ya yi daidai da wani hukuncin da kotu ta yanke a jihar Enugu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: