Kungiyar Bunkasa Tallalin Arzikin Kasahen Yammacin Afirka (ECOWAS), karkashin tawagar kula da shirye-shiryen zabe a Najeriya ta bayyana mahangarta game da zaben 2023 da za a yi.

Kamar yadda tawagar kungiyar ta bayyana, zaben na 2023 na iya shafar daukacin yankin Yammacin Afirka.
Tawagar ta bayyana hakan ne lokacin da ta ziyarci shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu a Abuja a farkon makon nan.

Tawagar ta ziyarci shugaban ne a karkashin jagorancin Tsohon Shugaban Hukumar zaben kasar Ghana, Kwadwo Afari-Gyan.

Da yake jawabi a madadin wakilan ,Daraktan Harkokin Siyasa na ECOWAS, Remi Ajiewa ya bayyana cewa yankin yammacin Afirka na neman ganin an samu sahihin zabe a Najeriya a 2023, domin shugaban Najeriya yana taka muhimmiyar rawa a yankin.
Ya ce sun san irin muhimmancin da Najeriya ke da shi a yankin Yammacin Afirka, hakan ya sa ko me ya shafeta ya shafi sauran ƙasashen daukacin Yammacin Afirka.
Mista Ajibewa ya kara da cewa sun zo Najeriya domin hada bincike gabanin zaben 2023.
Ya ce sashe na 11 da 12 da kuma13 na dokokin kungiyar ECOWAS ya tanadi cewa idan za a yi zabe za a hada rahoto ga dukkan mambobin kungiyar, musamman ma zaben shugaban kasa.