Hukumar kashe gobara ta Jihar Kano ta tabbatar da mutuwar wani mutum mai suna Habibu Mu’azu mai shekaru 45 a duniya bayan fadawa rijiya da yayi a kauyan ‘yan Dutse da ke cikin karamar hukumar Bichi a Jihar.

Mai magana da yawun hukumar Alhaji Saminu Yusuf Abdullahi ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a.

Saminu Yusuf ya ce hukumar ta samu labarin faruwal lamarin ne da misalin karfe 7:44 na safiyar Jiya Juma’a daga wani mutum mai suna Sunusi Abubakar.

Alhaji Saminu ya ce bayan sheda musu faruwal lamarin su ka aike da jami’an su gurin da lamarin ya faru.

Kakakin ya kara da cewa bayan ceto wanda ya fada rijiyar an tabbatar da mutuwar sa tare da mika gawarsa ga mai Unguwar kauyan na ‘Yan Dutse domin yi masa sutura.

Alhaji Saminu ya ce kawo yanzu jami’an su sun fara gudanar da bincike domin gano musabbabin faruwal lamarin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: