Kungiyar Dillalan Man Fetur ta Najeriya IPMAN ta bayyana cewa har yanzu ana kara ci gaba da fuskantar matsalar karancin Man Fetur a birnin tarayya Abuja da kewayanta duk da ambaliyar ruwan da ta haddasa cunkosan ababan hawa a Jihar Kogi taja baya.

Shugaban Kungiyar Debo Ahmad ne ya sanar da hakan a ranar Juma’a ya ce matsalar ta faro ne tun a farkon watan Oktoban da muke ciki inda aka samu dogayan layuka a gidajen man da ke birnin na Abuja da wasu yankunan da ke kusa da ita.

Hukumar da ke sanya ido a harkokin Man Fetur ta Najeriya NMDPRA ta bayyana cewa karancin Man da aka samu nada nasaba da ambaliyar ruwan da aka fuskanta.

Shugaban ya ce akwanakinnan ambaliyar ruwan ta ragu sosai amma har yanzu ana ci gaba da fuskantar matsalar karancin Man a birnin na Abuja.

Shugaban kungiyar ta IPMAN ya kuma alakanta matsalar karancin man ga kamfanonin da su ke dakon mai a Najeriya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: