Rundunar ‘yan sandan Jihar Katsina ta samu nasarar kama wani dillalin da ya ke safarar miyagun kwayoyi mai suna Ukashatu Idris mai shekaru 25 a Jihar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar SP Gambo Isa ne ya tabbatar da hakan a lokacin da ya ke ganawa da manema labarai a hedkwatar hukumar.

Gambo isa ya ce an kama wanda ake zargin ne tun a ranar 25 ga watan Oktoban da mu ke ciki a lokacin da su ka samu bayannan sirri.

SP Gambo ya kara da cewa jami’an rundunar sun kama wanda ake zargin ne akan titin Funtua zuwa Gusau a lokacin da ya ke dauke da busassun ganyayyaki na tabar wiwi har buhu 27 da sinki 31 na kwayar Exol da kuma sinki 30 na kwayar Tramadol.

Kakakin ya ce bayan kama wanda ake zargin ya amsa laifinsa tare da cewa ya kwaso ganyayyakin ne daga Jihar Edo zuwa Jihar Zamfara.

Gambo Isa ya kara da cewa wanda aka kama dan asalin kauyan Kiyaki ne da ke karamar hukumar Bungudu ta Jihar ta Zamfara.

Kakakin ya ce bayan kama wanda matashin ya sanar da sunan wani abokin sa Kabiru Master da ke Gusau wanda su ke safarar miyagun kwayoyin tare inda shima ake neman sa.

Kazalika Gambo Isa ya ce matashin ya shaida musu cewa kowanne buhu su na sayane akan kudi naira 30,00 daga bisa kuma su sayar akan kudi naira 60,000.

Leave a Reply

%d bloggers like this: